22 Maris 2026 - 13:30
Source: ABNA24
Irgc: Sama Da 200 Ne Suka Mutu Tare Da Raunata A Hari Kan Dimona Da Arad Da Eilat

A cikin jerin hare-haren da Iran ke kaiwa Isra’ila a jiya da dare gungun harin dakarun Irgc karo na 73 duk da karuwar matsin lamba kan tsaro da kan 'yan jarida Isra’ila mutane sama 200 ne suka mutu tare da jikkata ofishin Hulda da Jama'a na Irgc ya tabbatar da cewa: Kudu da Arewa na Isra’ila ya sha ruwan makamai a jerin yakin Wa’adi Sadiq 4 in da aka gudanar da harba wannan gungun na makamai da ramzin: "Ya Haidar (AS)" sadaukarwa ga jaruntakar shahidan tsaro, an harba wadannan makamai masu linzami da na'urori harba makamai ta dakarun juyin juya hali.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Wuraren sojoji da cibiyoyin tsaro a Arad, Dimona, Eilat, Beer-e-Saba, da Kriat Gat a kudancin yankunan Falasdinu da aka mamaye bayan rugujewar tsarin tsaron saman sojojin sahyoniyawa da sansanonin Ali Salim, Manhad, Al-Zafrah matattarar sojojin ta’addanci na Amurka suna daga cikin wuraren da wanna hari ya shafa.

An kai hari da anu’ikan makamai kamar su makamin Fattah, Qadr, Emad da jiragen yaki marasa matuka masu tarwatsa komai suka hara. Sama da mutane 200 ne aka ba da rahoton mutuwarsu da jikkata a farkon sa'o'in harin, a cewar rahotannin filin daga. Jami'an tsaro na sahyoniya sun kara matsin lamba kan 'yan jarida da shaidun gani da ido da su tantance barna da bayar da rahoton asarar rayuka.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha